Rashin lantarki ya sa daliban jami'ar ABU daina karatu

Harkokin karatu sun samu tangarda a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya yayin da dalibai suka shafe kusan wata daya zaune a gida sakamakon matsalar wutar lantarki da jami’ar ta shiga.

A ranar 15 ga watan Mayun da ya gabata ne hukumar da ke dakon hasken lantarki ta yanke hanyar lantarki ta jami'ar sakamakon bashin da suke bin jami'ar.

Jaridar Daily trust ta gano cewa hukumar gudanarwar jami'ar ta biya kamfanin Kaduna Electric Naira miliyan 40 daga cikin kudin wutar lantarki da ake bin su.

Sai dai duk da haka kamfanin na Kaduna Electric bai mayar da lanyin lantarkin makarantar ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post