Za mu dawo mulkin Kano ba dadewa - Ganduje


Gwamnan Kano mai barin gado Abdullahi Ganduje, PhDGwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce za su bar Gwamnati a jihar na dan wani lokaci amma za su dawo su amshi mulki ba da jimawa ba.
Ganduje ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi lokacin bikin bude aikin sabo titin kwanar Dala a karamar hukumar ta Dala.
“Tabbaas tarihi zai sake maimaita kansa na Dawo-dawo dama wancan Dawo-dawon din ma mu muka sa aka yi ta, Kuma mu muka san dawo-dawo, don haka a wannna lokacin ma kada mu manta da wakar nan ta Dawo-dawo” Inji Gwamna Ganduje.

Post a Comment

Previous Post Next Post