Zababben shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce duba da irin matsalolin da ke ci wa Nijeriya tuwo a kwarya a halin yanzu, da yiwuwar farkon mulkinsa ya dan yi tsauri. Sai dai Bola Tinubu ya ba 'yan Nijeriya tabbacin cewa cikin kankanin lokaci za a shawo kan wadannan matsaloli su fara darawa.
Bola Tinubu na magana ne a Abuja bayan kammala sallar Juma'a da yin adu'o'i a wani bangare na bukukuwa kafin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Zababben shugaban kasar da ya samu wakilcin mataimakinsa Kasshim Shettima ya ce akwai tarin matsaloli sannan ga kankanin lokaci da gare su na kokarin shawo kan wadannan matsaloli.
Category
Labarai