Abba Gida-gida ya bayyana kadarorinsa kafin fara aiki





Gabanin a yi bikin rantsar da shi a ranar Litinin, zababben gwamnan jihar Kano, Injiniya. Abba Kabir Yusuf ya bayyana ilahirin kaddarorin da ya mallaka da kuma bashin da ake bin shi a cikin wani kumshin takardu da ya mika a ranar Juma’a ga ofishin da'ar ma'aikata na jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa zababben Gwamnan wanda ya samu tarba daga Daraktar a hukumar ta CCB ta jihar Hajia Hadiza Larai Ibrahim, ya ce kwazonsa na bayyana kadarorin da ya yi nuni ne na gaskiya da rikon amana da zai zama ginshikin a gwamnati mai zuwa a jihar Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp