Dikko Radda ya nada sakataren gwamnatin Katsina da wasu mukamai 10Sabon Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Arch Ahmad Musa Dangiwa a matsayin sakataren gwamnatin jihar.

A cikin wata sanarwa da Dikko Radda ya sanya wa hannu, ta ce Gwamnan ya kuma nada Jabiru Tsauri a matsayin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati. Kazalika, sanarwar ta ce, Gwamnan ya nada Barr Mukhtar Aliyu a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, sai Abdullahi Aliyu Turaji a matsayin PPS.

Sauran nade-naden su ne na Malam Maiwada Danmalam a matsayin Darakta Janar mai kula da kafafen yada labarai, Sai Ibrahim Kaula Mohammed a matsayin mai magana da yawun Gwamna da Abubakar Badaru Jikamshi a matsayin mataimaki na musamman ga Gwamna kan kafafen yada labarai.

Post a Comment

Previous Post Next Post