Sarkin musulmi ya bayyana ranar Lahadi a matsayin ranar sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 bayan hijira

Sarkin musulmi ya bayyana ranar Lahadi a matsayin ranar sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 bayan hijira

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Lahadi 7 ga Yuli, 2024, a matsayin ranar farko ga watan Muharram, a daidai lokacin da aka shiga shekarar Musulunci ta 1446 bayan Hijira.


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar Sarkin Musulmi, Sambo Junaidu, a ranar ya fitar a ranar juma’a.


Ya bayyana cewa babu wani rahoton ganin watan da kwamitocin ganin wata na kasa da suka samu a fadin kasar.


Sanarwar ta ce, Kwamitocin ganin wata na kasa daban-daban a fadin kasar nan ba su samu rahoton ganin jinjirin watan Al-Muharram ba a ranar juma'a wato 29 ga watan Zulhijja shekara ta 1445 bayan hijira. Asabar 6 ga Yuli, ita ce 30 ga Zulhijja.

Sarkin Musulmi ya taya musulman Nijeriya murnar shiga sabuwar shekara,ya bukace su da su ci gaba da yi wa Nijeriya addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp