Kotu ta dage sauraron ƙarar da gwamnatin kano ta shigar kan sarautar Kano

Kotu ta dage sauraron ƙarar da gwamnatin kano ta shigar kan sarautar Kano

wata babbar kotu a jihar Kano ta dage ci gaba da zamanta har zuwa ranar 4 ga watan Yuli, inda za ta ci gaba da sauraren karar da gwamnatin Kano ta shigar tana bukatar tabbatar Sarki Sunusi na biyu a kejerar sarauta.


Babban lauyan gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar ta bakin Lauyan su Ibrahim Isah-Wangida suka shigar da karar a ranar 27 ga watan Mayu.


Suna neman a bada umarnin hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero da wasu sarakuna hudu da aka tube daga sarautar Bichi, Rano, Gaya da Karaye bayyana kansu a matsayin sarakunan gargajiya.


Sauran wadanda aka yi ƙarar su sun hada da Sufeto-Janar na ’Yan sanda, Daraktan jami'an tsaro na farin kaya a Jiha, da jami'an tsaro na Civil Defence da Sojojin Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post