Kungiyoyin da ke buga gasar firimiyar kasar Ingila sun amince a ci gaba amfani da VAR bayan kada kuri'a.
An kada kuri'a a wannan Alhamis din nan inda aka cimma matsaya a ci gaba da amfani da VAR din.
Kungiyar Wolves ce kadai ta zabi a daina amfani da VAR.