Majalisar dattawa a Najeriya ta tabbatar da ƙudirin dokar sauya taken ƙasa daga wanda aka saba.


Wannan na zuwa ne washe garin da ministan shari'a na ƙasar ya nuna buƙatar a ji ra'ayin sauran 'yan Najeriya kan wannan sauyi Na taken ƙasa wato national anthem a turance a lokacin da ya halarci taron jin bahasin masu ruwa da tsaki a harabar majalisar dokokin kasar.

Ƙudirin dokar ya wuce dukkan matakai da suka kamata a majalisun biyu na Najeriya wato ta wakilai da ta dattawa, abin da yanzu ya rage kadai shi ne sa hannun shugaban ƙasa.

Sai dai bisa kalaman ministan na Shari'a da yiyuwar a samu tsaiko wurin sanya hannun shugaban ƙasa kan dokar wacca ke buƙatar a koma amfani da tsohon taken Najeriya da aka maye gurbin sa a shekarar 1978.

Post a Comment

Previous Post Next Post