Magagin tsufa ne ke damun Obasanjo -Jamiyar APC

Jami'ya mai mulki a Nigeria wato All Progressive Congress ta bakin ɗaya Daraktan yãɗa labaran ta Bala Ibrahim ta yi raddi ga tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo bisa sūkar gwamnatin Tinubu da yayi cewa ba ta amfani da kuɗin tallafin man fetur ta hanyar da ta dãce.

Bala Ibrahim wadda ya baiyana Obasanjo a matsayin mai halin kunshe jama'a, ya ce alamun magagin tsufa sun fara baiyana daga Obasanjon wadda a cewar sa tun daga lokacin da ya rasa samun nasarar yin ta zarce a mulkin Najeriya wa'adi na uku ya ɗau gaba a zuciyar sa.

Ya ce wannan hali na Obasanjo ba yanzu ya fara a kan wannan gwamnati ta Tinubu ba saboda tsofin shugabanni irin su Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan bai bar su ba a zamanin da su ke mulki, sai dai ya baiyana cewa shi Obasanjo ne ma a zamanin mulkin sa ya rikirkita tattalin arzikin ƙasar.

A wata sanarwar da kakakin Obasanjo Kehinde Akinyemi ya fitar a 'yan kwanakin nan ne tsohon shugaban kasan ya ce koda ya ke matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka sun zama wãjibi, amma kuma gwamnatin tasa bata yin abin da ya dãce wurin aiwatar da matakan, musamman a ɓangaren sarrafa kuɗaɗen tallafin man fetur da ta cire.

Post a Comment

Previous Post Next Post