Mai karamin karfi a Nijeriya na bukatar sama da Naira 615,000 mafi ƙarancin albashi - Joe Ajaero

 Mai karamin karfi a Nijeriya na bukatar sama da Naira 615,000 mafi ƙarancin albashi - shugaban NLC Joe Ajaero

Kungiyar kwadago ta tabbatar da kudirin ta na biyan N615,000 mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar.

Shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) Joe Ajaero ya bayyana haka a jiya a ziyarar da ya kai hedikwatar kungiyar da ke Legas.

 

 Ajearo ya samu rakiyar wasu daga cikin  jami’an majalisar kungiyar ta jihar zuwa helkwatar kungiyar a birnin Legas, wadan da suka hada da shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE), Ambali Akeem Olatunji; Shugaban NLC na jihar Legas Funmi Sessi da kuma amintaccen NLC na kasa, Akporeha Williams.


Tawagar ta samu tarba daga manyan jiga-jigan editoci karkashin jagorancin Manajan Darakta/Babban Editan Victor Ifijeh.


Ajaero ya duk da cewa kungiyar kwadago ba ta adawa da batun biyan albashin ma’aikata da aka yi sulhu, amma tattalin arzikin da ke kan gaba ya sanar da matakin da ta dauka na gabatar da shawarwarin neman albashin N615,000 ga kwamitin sassa uku na gwamnatin tarayya kan mafi karancin albashi.


Yace al'ummar kasar nan na fama da wahalhalu da dama hakan yasa akwai bukatar ma'aikata susamu albashin da zai rage wahalhalu da ake ciki.

Post a Comment

Previous Post Next Post