Ba ma'aikacin da zai iya rayuwa da albashin kasa da N100,000 a Nijeriya - Shehu Sani

Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya bukaci gwamnatin Nijeriya da ta kawo karshen maganar mafi karancin albashi ga ma'aikatan gwamnati, inda ya yi nuni da cewa babu wani ma'aikacin da zai iya rayuwa a kasa da albashin N100,000 a wannan marrar rayuwar da ake ciki.

Sanata Shehu Sani na magana ne kan wa-ka-ci-wa-ka-tashin da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta NLC kan batun mafi karancin albashi ga ma'aikatan Nijeriya a tashar talabijin ta Arise.

Tsohon dan majalisar ya ce gwamnatin tarayya na da kudin da za ta iya biyan abin da ya dace ga ma'aikatan kasar, inda ya ce tsarin biyan kudin wadatacci da za su ishi ma'aikaci da gwamnati ke shirin yi, abu ne mai kyau.

Post a Comment

Previous Post Next Post