Sabon shugaban Senegal da zai yi fito-na-fito da Faransa

 


Daga ranar 02 ga watan Afrilu na 2024, kasar Seengal ta samu savon shugaba Bassirou Diomaye Faye da zai shiga fadar gwamnati ta matansa biyu. 

 A cikin abubuwan da ya lashi takobin yaƙa, Bassirou Diomaye Faye, ya hadar  da zargin  'Ɗaurin talala' da kasar Faransa ta yi wa tattalin arzikin ƙasarsa da ke Yammacin Afirka. Duk da cewa shuagaban Faransa Emmanuel Macron ya aike wa sabon shugaban da sakon taya murna, amma matashin bai janye alwashinsa na farko a yayin yakin neman zabe na cewa zai ceto kasarsa daga hannun Faransa a siyasance. 

Bassirou Diomaye Faye ya samu  kwarjinin cikin kankanin lokaci. Tsakanin nasararsa ta samu zama shugaban kasa da zaman gidan kaso, makonni 2 ne kacal, ya zama Daga wani gidan yari da ke Dakar zuwa fadar shugaban ƙasa.  Madugun adawar kasar Ousmane Sonko, ne ya  tsayar da shi ya maye gurbinsa a kasancewar shi Sonkon an haramta masa tsayawa takara. Faye da Sonko abokai ne na kud-da-kud, har ya raɗa wa ɗaya daga cikin 'ya'yan sunan Ousmane domin martaba abotarsu.

Rahoton bidiyo/murya: 


Bassirou Diomaye Faye da aka haifa a ranar 25 ga watan Maris na 1980 ɗan siyasar ƙasar Senegal ne kuma tsohon mai kula da lamurran haraji, shi ne  tsohon babban sakataren jam’iyyar PASTEF da aka rushe, matansa biyu sun hada da , Marie Khone Faye da Absa Faye. Marie Khone auren zumunci aka yi musu domin kuwa 'yar uwarsa ce, kuma ta haifa masa 'ya'ya huɗu, maza uku da mace ɗaya. Absa ba ta taɓa haihuwa ba.

Daye da shi da matansa biyu

A shekarar 2000, Faye ya yi jarabawarsa ta Baccalaureate kwatankwacin jarabawar WAEC a Nijeriya. Ya yi nasarar kammala karatun digiri na biyu a bangare karatun lauya sannan ya cinye jarabawar guda biyu, ya shiga makarantar koyon sha'anin mulki ta kasar ENA a takaice sai kuma majistare a 2004. Bayan ya kammala, sai Faye ya zaɓi zama jami'in haraji a sashen haraji da rukunin gidaje, inda abotarsu ta ƙullu da Sonko, wanda makaranta ɗaya suka yi.

A 2014, dangantakar Faye da Sonko ta yi ƙarfi, suka zama kud-da-kud a ƙungiyar haraji da rukunin gidaje wato Taxes and Estates Union da Sonko ya kafa.

Bayan kasancewa cikin halin rashin tabbas a tsayawa takarar Sonko a zaɓen na shugaban ƙasa. Jam’iyyar PASTEF ta zaɓi Faye a watan Nuwamba na 2023 a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen na 2024, duk da ana tsare da shi. Sai da an rushe PASTEF watannin baya, da ke nuna cewa yana takara ne a matsayin ɗan takara indifenda.

A ranar 20 ga watan Janairu na 2024, Majalisar Tsarin Mulki ta Senegal ta wallafa jerin sunaye na ƙarshe na 'yan takarar shugaban kasa, kuma ba sunan Sonko a ciki. Bayan shari'a daban-daban, aka wanke Sonko cewa zai tsaya takara tun da kotu ba ta taɓa samun sa da wani laifi ba, kodayake yana ci gaba da zama a tsare. Dandanan Sonko ya sanar da goyon bayansa ga Faye a zaɓen.

A lokacin yaƙin neman zaɓe Faye ya ɗauki alƙawarin samar da ayyukan yi, ya yi yaƙin neman zaɓe ba ƙarami ba a kan zai yaki rashawa, ya kuma lashi takobin sake duba kwagilolin makamashi. Taken takararsa shi ne "Diomaye mooy Ousmane" da ke nufin "Diomaye Ousmane ne" a Wolof, kuma yake fatar kwarjini irin na Sonko da kuma samun karɓuwa da matasan Senegal za su ƙarfafa gangaminsa. Tsare-tsaren Faye sun yi kama da na Sonko a takarar da ya yi a shekarar 2019.


Shugaba Tinubu na Nijeriya tare da Faye

A ranar 14 ga watan Afrilu na shekarar 2023, aka kama Faye a lokacin da yake hanyarsa ta fita daga ofishinsa na haraji da ke a birnin Dakar. Daga nan a ka miƙa shi a hannun 'yan sanda ana tuhumarsa da "yaɗa labarun ƙarya, da ƙin bin umarnin kotu, da ɓata sunan hukuma" biyo bayan wasu rubuce-rubucen da ya yi a soshiyal midiya. A wannan rubutu ya yi Allah wadai da rashin adalcin da ya ce ana aikatawa a tsarin shari'a na ƙasar. Ana ci gaba da haka aka ƙara wasu tuhume-tuhumen na 'tunzura jama'a da tauye lamurran tsaro na ƙasa da suka sa aka tsare shi.

Bayan wani yunkuri da tsohon shugaban ƙasa Macky Sall ya yi a watan Fabrairu na ɗage zaɓukan, da dalilan ba a warware taƙaddamar wane ne zai tsaya kara ba, aka soma bore da zanga-zanga, inda Kotun  Tsarin Mulkin ƙasar ta soke ɗagewar.

Faye ya ce ya yi imani da tsari na sauyi da kuma gwagwarmayar kishin Afirka domin ƙwato ɗiyaucin Senegal, taken da wasu masu nazarin lamurra suka yi imanin manufa ce ta nesanta ƙasar da Turawan Yammacin Turai musamman tsohuwar ƙasar da ta musu mulkin mallaka Faransa


Akkufo-Addo tare da Faye

Faye ya ɗauki alƙawarin rage ƙarfi da ikon shugaban ƙasa, da maido da tsarin mataimakin shugaban ƙasa.

Tun kafin a zabe shi, Faye ya ce zai  fifita,  yaƙi da siyasar rashawa idan aka zabe sa matsayin shugaban ƙasa, inda ya ce babu wata ƙasa da za ta iya ci gaba idan rashawa da almunbazzaranci da dukiyar jama'a suka zama ruwan dare a kasar te Senegal mai mutane miliyan 18.

Post a Comment

Previous Post Next Post