Ni ba uban gidan kowa ba ne a siyasar jihar Kaduna - Elrufa'i
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce ba ya son a yi masa kallon ubangidan kowa a siyasar jihar Kaduna.
Elrufa'i ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna ilimi ga manyan jami’an gwamnati a jihar Borno, ranar Litinin.
Ya ce sau biyar kacal ya ziyarci jihar ta Kaduna tun bayan da ya bar mulki kusan shekara daya da ta wuce.