An lissafto Sanatocin Katsina da Kano da ba su gabatar da kudirin doka a zauren majalisa ta 10 ba


Daga cikin Sanatocin kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya nuna, akwai Sanata Rufa'i Hanga da ke wakiltar Kano ta tsakiya da Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua da ke wakiltar Katsina ta tsakiya da Sanata Muntari Dandutse da ke wakiltar Katsina ta Kudu.

Kazalika binciken ya gano tsoffin Gwamnoni 4 da ke zauren majalisar yanzu haka da ba su gabatar da kudirin doka ko daya ba tun da aka rantsar da majalisar, daga cikin akwai Abdul'aziz Yari daga jihar Zamfara, Adams Oshimhole daga jihar Edo da Simon Lalong daga jihar Plateau.

A majalisa ta 10 dai akwai tsoffin Gwamnoni 13 da suka yi nasarar zama sanatoci bayan sun kammala wa'adin mulkinsu na gwamnoni. Daga cikinsu akwai shugaban majalisar dattawan Godswill Akpabio daga Akwa Ibom da Abdul'aziz Yari daga jihar Zamfara da Aliyu Wamakko daga Sokoto da Aminu Tambuwal daga Sokoto.

1 Comments

  1. Ta wace hanya ake samun damar zantawa da ku

    ReplyDelete
Previous Post Next Post