Farashin man Disil a Nijeriya ya sauka zuwa N1,225 kan kowace lita


 Farashin man Disil a Nijeriya ya sauka zuwa N1,225 kan kowace lita bayan kamfanin Dangote ya fara sayar da shi yayin da za su fara sayar da man fetur a cikin watan Mayun bana.

A ranar Talatar da ta gabata ce matatar mai ta dala biliyan 20 ta fara fitar da man dizal zuwa kasuwannin cikin gida a ranar larabar da ta gabata.


Inda ta sayar da mafi ƙarancin lita miliyan ɗaya ga kowane ɗan kasuwa mai rijista da ya samu dama daga kamfanin tun lokacin da ta fara sayar da gas.


Wasu jami’an kamfanin da dillalan man fetur sun tabbatar da cewa an raba wa ‘yan kasuwa kayayyakin a tsakanin N1,225 akan kowacce lita zuwa Naira 1,300.


 kamfanin yace yana saran cigaba da raba gas din zuwa ciki da wajen kasar nan da kuma fara sayar da man fetur a watan mayun shekarar nan.


Shugaban kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya, Abubakar Maigandi, ya shaida manema labarai cewa 

sun fara fitar da dizal ga ‘yan kasuwa tun makon da ya gabata. sun kuma yi alkawarin sayar da man jiragen sama nan ba da jimawa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp