Emefiele ya yi amfani da N18bn wajen buga sabbin kudi N684.5m - EFCC


 Emefiele ya yi amfani da N18bn wajen buga sabbin kudi N684.5m - EFCC Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta sake shigar da Emefiele kara kan sabuwar tuhuma da take yi masa na amfani da zunzurutun kudade da yawansu ya kai N18bn waje buga sabbin kudi N684.5m


EFCC ta shigar da karar ne a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.


A cikin takardar tuhumar da aka fitar a ranar Talata, EFCC ta yi zargin cewa Emefiele ya karya doka da nufin cutar da jama’a a lokacin da yake aiwatar da manufar musanya Naira a lokacin mulkin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Post a Comment

Previous Post Next Post