'Yan bindiga sun hallaka shugaban jam'iyyar APC a Katsina

Wasu mahara da har lokacin hada wannan labarin ba a tabbatar da adadinsu ba, sun bindige Malam Sai'idu Jikan Basa wanda shi ne shugaban jam'iyyar APC na mazabar Mai Dabino ta karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

Majiyar DCL Hausa ta tabbatar mata da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:37 na yammacin Larabar nan a kan hanyarsa daga Danmusa zuwa Mai Dabino.


Bayanai sun ce an kira jiga-jigan jam'iyyar APC na karamar hukumar Danmusa zuwa wani taro a hedikwatar karamar hukumar, inda daga kauyen Mai Dabino ya tafi Danmusa don halartar wannan taro.

Yana kan hanyarsa ta komawa Mai Dabino bayan kammala taron, wannan ibtila'in ya faru da shi, da wani mutumin kauyen Kokarawa da ya rago wa hanya zuwa kasuwar Mai Dabino da ke a ranar Larabar nan.

Majiyar ta ce an yi musu jana'iza bayan sallar la'asar din nan da yammacin Laraba.

Kauyen Mai Dabino na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro da ba su iya shiga hedikwatar karamar hukumar Danmusa sai sun zagaya ta karamar hukumar Kankara.

Post a Comment

Previous Post Next Post