Ba mu ciyo sabon bashi ba - Gwamnatin Katsina

 Ba mu ciyo sabon bashi ba - Gwamnatin Katsina 


Gwamnatin jihar Katsina ta musanta ikirarin da ofishin kula da basussuka, DMO, ya yi cewa gwamnatin jihar ta ciyo sabon bashi.

A wani rahoto da Ofishin kula da basussuka ya wallafa kwanan nan ya bayyana cewa jihar Katsina karkashin Gwamna Radda tare da wasu jihohin Nijeriya sun karbo sabon lamuni, domin cike gibi da aiwatar da wasu ayyuka da za su yi.


Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Dikko Radda, Ibrahim Kaula Mohammed, ya aike wa DCL Hausa, ta musanta rahoton wanda ta ke cewa a halin yanzu jihar ba ta ciyo wani sabon bashi ba.


Sanarwar ta ci gaba da cewa babu wani sabon lamuni da gwamnatin Katsina a yanzu ta karba a karkashin Gwamna Radda amma wannan ba yana nufin gwamnatin jiha ba za ta ci bashi ba a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, za ta iya karbar bashi domin inganta rayuwar al’ummarta da ma jihar baki daya.


Sanarwar ta ce gwamnatin jihar na iya kokarinta wajen ganin ta bijiro da sabbin ayyuka da za su inganta rayuwar al'ummar jihar baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp