Jose ya kammala aikin horar da tawagar kungiyar Super Eagles
Kocin tawagar kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya wato Super Eagles Jose Peseiro ya sanar da cewa ya kawo karshen aikinsa na horar da tawagar ta Super Eagles.
Jose wanda ɗan asalin kasar Portugal ne ya bayyana hakan ne a shafinsa na X da a ranar Juma'ar nan.
"A jiya muka kawo ƙarshen kwantaragin da na kulla tsakanina da Hukumar Kwallon ƙafa ta Nijeriya NFF." Inji Jose