Fursuna ya kwace bindigar Gandiroba ya harbi wani mai faci a Kwara

 

Fursuna ya kwace bindigar Gandiroba ya harbi wani mai faci a Kwara


Wani fursuna a gidan yari da ke Oke-Kura a Ilorin babban birnin jihar Kwara ya yi kukan kura ya kwace bindiga hannun jami’in tsaron gidan yari ya harbe wani wani mai sana'ar faci a gefen hanya.

Hakan ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da aka fitar da wasu fursunonin gidan yarin.

Lamarin dai ya faru ne misalin karfe 8:00 na safe, kuma ya haifar da firgici da fargaba yayin da mazauna yankin suka tarwatse domin samu tsira a yayin faruwar qbin wanda ya yi kama da wasan kwaikwayo.

Nan take aka garzaya da mai facin zuwa wani asibiti domin kula da lafiyarsa aka kuma ci gaba da tsare wannan fursuna da ya yi aika-aika.

Post a Comment

Previous Post Next Post