APC ta zabi Idahosa a matsayin mataimakin gwamnan Edo a zaben da yake gabatowa

 APC ta zabi Idahosa a matsayin mataimakin gwamnan Edo a zaben da yake gabatowa.


Jam’iyyar (APC) ta tsayar da Hon. Dennis Idahosa a matsayin mataimakin dan takarar gwamna a zaben gwamnan Edo da za a yi ranar 21 ga watan Satumbar shekarar da muke ciki.


Shugaban jam’iyyar APCn na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da sakataren jam’iyyar na kasa, Sen. Ajibola Bashiru za su gabatar da Sanata Monday Okpebolo, a matsayin dan takarar gwamnan da kuma abokin takararsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a villa dake Abuja.


Idahosa shine ya maye gurbin Hon. Omoregie Ogbeide-Ihama wanda dan takarar gwamnan ya bayyana a makon da ya gabata a matsayin abokin takararsa.


Jaridar Nation ta rawaito cewa Idahosa, dan majalisar wakilai, an tabbatar dashi a daren ranar Lahadi bayan wani dogon zama da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Edo, da shugabannin jam’iyyar da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima suka yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post