Kotu tabayar da belin Abdulmajeed Dan bilki kwamanda bisa wasu sharruda.


Wata kotu dake zaman ta a Kano, ƙarkashin jagorancin mai shari’a Abdulaziz Habib, ta bayar da belin Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda bisa wasu sharuddan.

Sharuɗan belin sun haɗa da gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa, Hakimi a Kano ko Sakatare na din-dindin ko kuma bayar da Naira Miliyan daya idan ba'a samu wadannan mutane ba.

Daga bisani an ɗage shari'ar zuwa ranar 26 ga wannan watan da muke ciki na Fabrairu.

An dai tsare fitaccen dan siyasar ne kan kalaman batanci da ya yi wa tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.


Post a Comment

Previous Post Next Post