Hukumomin mulkin sojan Nijar sun dakatar da kungiyar 'yan jaridu ta kasa


 

Ministan cikin gidan Nijar  janar Toumba ya dauki wannan mataki a cikin wani kudurin doka da ya saka wa hannu a ranar 29 Janairun wannan shekara ta 2024 inda a ciki ya sanar da rushe wannan kungiya har sai baba ta gani


Ko da yake ministan bai sanar da dalilansa ba na daukan matakin amma ya maye gurbin membobin nata da sakatarorin ma'aikatar sa da ta sadarwa wadanda za su jagorancin aikin kungiyar na wani lokaci


To amma sai dai shugaban kungiyar ta Maison de la Presse Ibrahim Harouna ya ce basu da labarin wannan mataki domin kuwa basu samu takarda a hukumance da ta dakatar da ayyukan nasu duk kuwa da yadda take yawo a shafukan sada zumanta na zamani

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp