Kotu ta bayar da belin Murja 'yar Tik-tok 

 


Sabanin jita-jitar da ake ta yadawa cewa fitacciyar jarumar Tiktok, Murja Kunya ta tsere daga gidan yari, kakakin gidan gyaran hali na Kano, Musbahu Kofar Nassarawa ya ce an sake ta ne biyo bayan umarnin kotu.

Kofar Nassarawa ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa an sake ta tun ranar Alhamis.


 "Kotu ce ta kawo mana ita domin a ci gaba da tsare ta, kuma kotun ce ta ba mu umarnin mu sake ta," in ji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post