Da bukatar NAHCON ta dauki tsattsauran mataki kan 'yan damfara - IHR

Kungiyar nan mai zaman kanta da ke ba da rahoton ayyukan hajji da Umrah ta Independent Hajj Reporters IHR ta ja hankalin hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON da ta kama tare da gurfanar da duk wanda suka kama da laifin damfara da ke yada labaran da ba su inganta ba.

Shugaban kungiyar Alhaji Ibrahim Muhammad a cikin wata sanarwa da ya aike wa DCL Hausa, na martani ne kan wata sanarwa da aka yi ta yadawa cewa hukumar NAHCON na daukar ma'aikata musamman na lafiya da 'yan jarida da za su yi aikin wucin-gadi a aikin hajjin shekarar nan 2024.

Kungiyar ta yaba da yadda hukumar NAHCON ta gaggauta fitar da sanarwar musanta wannan labari. Sannan kungiyar ta karfafi guiwar hukumar NAHCON da ta bi diddigi don kamo wadanda suke kitsa wannan bahallatsa.

IHR ta tunaso cewa ko a aikin hajjin shekarar 2023 da ya gabata, sai da aka samu wasu bata-gari suka kirkiri wani shafi suka rika tura wa mutane cewa su cika Yariman Saudiyya ya dauki nauyin aikin hajji ga 'yan Nijeriya a kyauta. Sai dai ko a lokacin sai da aka bi diddigi aka gano, ashe wasu ne a jihar Oyo suka kitsa wannan kitimirmira.

Post a Comment

Previous Post Next Post