"Ba mu ga dalilin da zai sa Tinubu ya yi murabus " martanin APC ga PDP

 

"Babu dalilin da zai sa Tinubu ya yi murabus" martanin APC ga PDP

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya dage cewa shugaban kasa Bola Tinubu ba zai yi murabus ba saboda halin kuncin da tattalin arzikin kasa ke ciki.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Rabiu Ibrahim ya sanya wa hannu, yayin da yake mayar da martani ga gwamnonin jam’iyyar PDP da suka yi kira ga shugaban kasar da ya yi murabus saboda halin kuncin da kasar ke ciki.

A cewarsa, kiran da gwamnonin jam’iyyar adawa suka yi ba wani abu ba ne illa wani yunkuri na karkatar da hankalin jama’a da ya kamata su shagaltu da goyon bayan kokarin shugaban kasar na kawo saukin tattalin arziki ga al’ummar Nijeriya.


Post a Comment

Previous Post Next Post