Sanusi Lamido ya goyi bayan mayar da wasu sassan CBN zuwa Lagos

 

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma sarkin Kano na 14 Sanusi Lamido Sanusi ya goyi bayan gwamnatin tarayya a shirin da take yi na mayar da wasu sassan babban bankin CBN kasar zuwa birnin Lagos.

 

Yayin da yake mayar da martani kan masu sukar tsarin, Sanusi ya ce abinda suke yi abu ne mai matukar hadari ga makomar bankin, don haka gatan da za’a yi masa kadai shine mayar da shi jihar Lagos.

 

Sarki Sunusi mai murabus ya kuma ci gaba da cewa masu wannan suka musamman ma’aikatan bankin ba kowa bane illa karnukan farautar ‘yan siyasa masu samun kudade da babban bankin, don haka akwai bukatar su yi gaggawar daina sukar gwamnati.

Ya ce mayar da sassan bankin zuwa Lagos zai saukaka aiki, da kuma rage kashe kudaden gudanarwa da ake yi kowacce rana.

Sai dai ya ce akwai bukatar sassa irin su, fannin tsara dubarun tattalin arziki, ofishin mai binciken kudi, da ofishin takaita asara da sauran sassa da ke aiki kai tsaye da ofishin gwamnan bankin su ci gaba da zama a Abuja.

Post a Comment

Previous Post Next Post