Sanata Ike Ikweremadu ya share watanni 9 cikin daurin shekaru 9 da kotu ta yi masa a Ingila

A cikin watan Mayun shekarar 2023 ne dai wata kotu a kasar Ingila ta yanke hukuncin daurin shekaru 9 ga tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Ike Ikweremadu.

Kotun dai ta kuma yanke wa mai dakin Sanata Ike da karin wani mutum daya hukunci duk bayan an same su da laifin safarar wani matashi don harkallar kodar da za a sanya wa diyarsu.

Sanata Ike Ikweremadu mai shekaru 60 da matarsa Beatrice mai shekaru 56, sun dade suna fafutukar yadda za su samar wa diyarsu Sonia mai shekaru 25 koda.

Kotun ta same su da laifin safarar sassan jikin bil'adama.

Beatrice, matar Ikweremadu ta samu hukuncin daurin shekaru 4 a yayin da mutumin da zai ba da kodar aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 10.

Sanata Ike Ikweremadu dai da ya fito daga jihar Enugu, ya fara zuwa majalisar dattawan Nijeriya daga shekarar 2003. Dan jam'iyyar PDP, Ike ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya sau uku a jere a majalisa ta 6,7 da 8.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp