Sadiya Umar Faruq za ta gurfanar a gaban EFCC

Tsohuwar minista jin kai a lokacin mulkin Shugaba Buhari Sadiya Umar-Farouq za ta gurfana a gaban jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) bisa zargin almundahanar kudi har naira biliyan 37.

A makon jiya ne dai EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar domin ta amsa tuhume-tuhume da ake yi mata lokacin da ta ke rike da mukami.

Ana tuhumar ta kan zurarewar wasu kudade kimamin N37,170,855,753.44 da ake zargin an karkatar da su a yayin da ta ke jagorancin ma'aikatar ta jin kai.

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun shaida wa wakilin majiyar DCLHausa ta Daily trust a ranar Talata cewa, an bukaci tsohuwar ministar ta bayyana a gaban masu bincike a hedikwatar hukumar ta EFCC da ke Jabi, Abuja, da karfe 10:00 na safiyar Larabar nan.

Post a Comment

Previous Post Next Post