Hisbah a Kano ta kama mota makare da barasa
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sanar da kama wata babbar mota makare da kwalaben barasa.
Hukumar ta kama motar a hanyar Zariya, ta kuma kama direban motar da wasu mutane biyu.
Babban Daraktan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Alhaji Abba Sufi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Malam Ibrahim-Fagge ya sanya wa hannu a Kano.
“ Yace Motar da ke dauke da kwalabe daban-daban na barasa sama da 24,000 an kwace daga hannun ‘yan sumogal a hanyar Zariya da tsakar dare.
Jami'an Hisbah a jihar sun himmatu wajen yaki da shan miyagun kwayoyi da fasakwaurin barasa da sauran abubuwa masu sa maye a cikin jihar.