Majalisar Dattawa zata gayyaci Wike kan matsalar tsaro a abuja.

 Majalisar dattawa za ta gayyaci Wike kan matsalar satar mutane a abuja. 




Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya abuja, Ireti Kingibe, ya ce majalisar dattawa za ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, kan karuwar rashin tsaro da ayyukan ta'addanci a Abuja.


Kingibe, ya bayyana hakanne yayin zantawarsa da manema labarai a jiya Lahadi inda ya bayyana cewa Majalisar Dattawa za ta gayyaci Wike da shugabannin hukumomin tsaro kan yawaitar laifuka a abuja.


Yace, Lokacin da Majalisar Dattawa ta dawo aiki, an shirya cewa kwamitin (Majalisar Dattawa) na bukatar ya zauna da ministocin biyu da hukumomin tsaro domin su basu tsare-tsarensu na tsaro domin Kawo Karshen matsalar tsaron a abujar. 


wannan shi ne tsarin da ake gani zai kare al’ummar babban birnin tarayyar abuja. domin da ministan abuja, Kwamishinan yansanda da shugaban DSS, Yakamata suyi tsari maikyau wajen kawarda  Matsalar tsaro a yankin. 


 

Post a Comment

Previous Post Next Post