Gwamnatin tarayya ta mayar wa da sanata Ali Ndume martani game da kalaman da yayi da ke nuni da cewa gwamnatin na kullawa ‘yan arewa wata makarkashiya, shine ma dalilin da ya sa zata mayar da wasu sassan CBN da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama zuwa jihar Lagos.
Ta cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce wannan
ba komai bane illa yunkurin tunzura ‘yan arewa a kan ‘yan kudu, kuma ba zai yi
nasara ba.
Kalaman na Sanata Ndume sun biyo bayan sanarwar
gwamnati na mayar da wasu sassa masu muhimmanci na babban bankin kasa CBN da
kuma hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama zuwa jihar Lagos ba tare da
bayar da wani gamsashen dalili ba.
Tun bayan fitar wannan labari ne ‚yan arewa ke mayar
da mabanbantan martani, yayin da wasu ke ganin wannan ba komai bane illa
yunkurin mayar da arewa saniyar ware, inda kuma wasu ke da ra’ayin cewa hakan wani
salo ne na shirin raba kasar.
Baya
ga wannan an kuma zargi gwamnatin ta Tinubu da yunkurin mayar da fadar shugaban
kasa kachokan zuwa jihar Lagos, sai dai tuni gwamnatin ta musanta wannan zargi.