Kasar Bénin ta sanar da dage matakin daina karbar hajojin Nijar a tashar jirgin ruwan ta

A cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun babban daraktan tashar jirgin ruwan Cotonou Bart Jozef Johan VAN EENDO kasar Benin ta sanar da dage matakin nata na daina karbar hajojin Nijar a tashar tata

Kasar ta Bénin dai ta dauki matakin dakatar da karbar hajojin na 'yan Nijar a tashar ruwan tata tun a ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata

Wannan mataki na hukumomin Bénin din na zuwa ne 'yan kwana kadan bayan da aka jiyo shugaba Patrice Talon yana bukatar kawo karshen tsamin dangantakar daga tsakanin kasar tasa da kasashen da ke karkashin mulkin soja da ke cikin yankin kungiyar ECOWAS

Post a Comment

Previous Post Next Post