Tsohuwar ministar jin kai a Nijeriya Sadiya Umar Faruq, ta nesanta kanta daga wasu rahotanni da ke alakanta ta da wani dan kwangila James Okwete da aka ce ya yi zargin tana da hannu a wata badakalar kudi a ma'aikatar jin kai ta Nijeriya.
Sadiya Umar Faruq a cikin wata sanarwa da ta wallafa a sahihin shafinta na Facebook, ta ce kwata-kwata ba ta ma san mai wannan sunan ba, bare ma a ce wata alaka ta taba hada su.
Jaridar Punch ta rawaito cewa akwai wani dan kwangila mai suna James Okwete da hukumar EFCC ta kama, yake ba ta bahasin cewa tsohuwar ministar Sadiya na da hannu a wata badakalar kudi Naira bilyan 37 tare da wasu daraktocin da suka yi aiki a ma'aikatar a lokacin tana minista.
Har ma hukumar ta ce da yiwuwar a kama ita tsohuwar ministar da wadancan daraktoci da wannan dan kwangila ya ayyana.
A cikin sanarwar Sadiya Umar Faruq,vta ce har yanzu tana mai matukar farinciki da bugun kirjin yadda ta yi aikinta na minista cikin tsanaki da tsafta ta hidimta wa kasar ta ba tare da wani son rai ya shigo ba.
Ta ce ta tuntubi tawagar lauyoyinta don bullo ma lamarin ta hanyar da ta dace.