Zubar da mutunci ne dan sanda ya rika karbar N100 daga hannun direbobi

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi, ya caccaki jami’an da ke karbar Naira 100 a kan hanya daga hannun masu ababen hawa, inda ya ce jami'an da suke aikata haka suna zubar wa da kansu mutunci ne.

A cewarsa ya kamata ‘yan sandan da ke yin wannan aika-aika su daina saboda suna cin hanci da rashawa.

Adejobi ya bayyana hakan ne a yayin da yake mayar da martani ga wani mai amfani da shafin Tuwita (X) wanda ya tambayi dalilin da ya sa ‘yan sanda ke karbar Naira 100 daga masu amfani da hanyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post