Sanannen mawakin siyasar nan a arewacin Nijeriya Dauda Adamu Abdullahi da aka fi sani da Rarara ya ce gwamnatin da ta gabata ta tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ta lalata kusan kowane bangare na kasar.
Rarara a wata ganawa ta musamman da manema labarai a Kano, ya ce ya ba gwamnatin ta Buhari shawarwari daban-daban na yadda za ta inganta ayyukanta, amma ba ta dauki shawara ko daya daga bangare na ba.
Mawakin da ya yi jawabi mai kama da ya dawo rakiyar gwamnatin da ta shude, ya nuna kamar yana nadamar irin goyon bayan da ya bata.
Ya yi karin hasken cewa bai samu sisin-kwabo a gwamnatin Buhari ba, ya kara da cewa duk wanda ya ke da hujjar cewa ya samu kudi gwamnatin Buhari ya zo ya nuna.
Ta fuskar ba da gudunmuwa a wajen kafa sabuwar gwamnatin Tinubu kuwa, mawaki Rarara, ya ce tsoffin gwamnonin Katsina Aminu Masari da na Kano Abdullahi Ganduje ne kadai za su iya hada kafada da shi wajen tallafar nasarar gwamnatin Tinubu arewa.
Sai dai Dauda Adamu ya yi karin hasken cewa akwai makiya Tinubu da aka nada mukamai daban-daban a gwamnatinsa.