Kotun da ke sauraren kararrakin da suka shafi haraji da ke zamanta a Lagos ta umurci kamfanin sadarwa na MTN da ya biya gwamnatin kasar kudin da suka kai Dalar Amurka milyan 72,551,059 kwatankwacin Naira bilyan 57.5 (idan an sayar da Dalar kan kudi Naira 795).
An dai umurci kamfanin ya biya wadannan kudaden da aka yi lissafin ba a biya ba daga shekarar 2007 zuwa 2017 ta hannun hukumar tattara kudaden haraji ta FIRS.
Sai dai kotun ta sahale wa kamfanin da kada ya biya Dala milyan 21,039,807 daga cikin kudin a matsayin kudin ruwa da kuma na jan kafa.
Tawagar alkalai biyar, karkashin jagorancin Prof A.B Hamed ne suka yanke wannan hukunci bayan da hukumar FIRS ta gabatar da koken hakan gaban kotu.