'Yan ta'adda sun kashe mutane 6 a wani sabon hari a Dansadau jihar Zamfara

Wasu mutane dauke da muggan makamai sun mamaye tare da kashe mutane kusan 6 a kauyen Dansadau na karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

A ganawar da Radio Nigeria ya yi da wasu shaidun gani da ido, sun sanar cewa barayin dajin sun kai hari a kauyen da misalin karfe biyu na ranar Talata, a lokacin da mutanen ke sallar azahar.

Rahotanni sun ce mutanen sun je kauyen bisa babura dauke da makamai su na harbin kan mai uwa da wabi, suka kashe mutanen tare da sace daya.

Shaidun suka ce 'yan ta'addar sun fara harbi a tashar mota, sai suka fantsama zuwa kasuwa suna harbe-harbe suka jikkata da dama.

Bayanai sun ce mutane kusan 4 sun samu raunuka inda suke karbar magani a babban asibitin Dansadau.

1 Comments

Previous Post Next Post