An gurfanar da matar da ta caka wa wani mutum almakashi a Kano

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Gama ta jihar Kano ta tasa keyar wata mata mai suna Hafsa Musa a gidan gyaran hali bisa zarginta da daba wa wani mutum mai suna Buhari Mikail da almakashi.

'yan sandan sun shaida wa kotun cewa wadda ake kara ta aikata laifin ne a lokacin da fada ya barke tsakanin kawarta da mutumin inda ta daba wa masa almakashin ya kuma yi masa mummunan rauni.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare ta a gidan yari tare da dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Satumba domin yanke mata hukunci.

Post a Comment

Previous Post Next Post