Na kyautata rayuwar talaka a mulkina - Buhari


                                                   Shugaba Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari ya ce mulkinsa na shekaru takwas ya kyautata rayuwar talakawa a kasar. A jawabin bankwana da ya yi Nijeriya a ranar Lahadi ya ce mulkinsa ya taimaka wa mutanen da ke a yankunan karkara da sauran marasa karfi bunkasa rayuwarsu. 

Ya ce ya yi iyakar kokarinsa wajen yaki da cin hanci da rashawa, inda ya ce ya kwato kudade masu yawa daga hannun barayin gwamnati domin kyautata rayuwar 'yan Nijeriya.

'' Na gamsu cewa na dora Nijeriya a hanyar da ta dace, na kuma gamsu cewa zan bar Nijeriya fiye da yadda na tarar da ita a 2015'' in ji Buhari

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp