'Yan bindiga sun kona mota dauke da kudi a kauyen Katsina

Wasu 'yan bindiga da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun banka wuta ga wata mota kirar Golf da ke dauke da 'yan kasuwa na kauyen Mai Dabino da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce motar na dauke da fasinjoji ne da za su tafi Kano domin saye-saye. Majiyar DCL Hausa ta ce 'yan kasuwar sun yi nasarar ficewa daga cikin motar, amma kuma ba su iya samu suka tsira da kudade da kadarorin su da ke cikin motar ba.

Majiyar ta ce daga cikin fasinjojin akwai wani dan kasuwa da ya ke dauke da kudin da suka kai Naira dubu 300, da ya kulle don zuwa Kano sayayya musamman ganin yadda sallah ta gabato.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 7:30 na safe zuwa 8am a kan hanyar Mai Dabino zuwa Gurbi ta karamar hukumar Kankara a jihar.

Majiyar DCL Hausa ta shaida mata cewa yanzu hanyar Mai Dabino zuwa Danmusa a isa garin Yantumaki ta gagare su, shi ne suka koma bi ta hanyar Gurbi zuwa Kankara, nan ma 'yan bindigar sun gano, sun fara tare su.

Majiyar ta ce 'yan bindigar ba su yi nasarar tafiya da ko dan kasuwa daya ba, amma dai sun yi awon gaba da wani mutum dan asalin karamar hukumar Mani da ya je kauyen ziyarar ta'aziyya.

Majiyar ta ce lokacin da suka ji karar harbin bindiga, suka yi kokari suka juya suka koma da suka samu suka tsira da kyar, mota kirar Golf da ke gaba, ita ce ba a iya samu aka juya da ita ba sai dai mutanen ciki suka fita suka tsere, da barayin dajin suka zo, suka banka mata wuta.

Kan haka majiyar ta yi roko ga gwamnati da sauran hukumomin tsaro da su kawo musu daukin gaggawa ganin irin halin da suke ciki na rashin tabbas a yankin nasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post