Kotu ta ci tarar Gwamna Abba N25m game da shari'ar Alhassan Doguwa

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ci tarar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Naira miliyan 25 kan haddasa rudani da damuwa ga dan majalisar tarayya mai wakilta Kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Hon Alhassan Ado Doguwa.

Hakazalika, kotun ta kuma soke umurnin da gwamnan ya ba Atoni-Janar na jihar na sake duba shari’ar Alhassan Doguwa kan zargin kisa.

A zaman kotun na ranar Juma'a, Mai Shari’a Donatus Okorowo, ya umurci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da kada ya sake taba ’yancin dan'Adam na mai kara Alhassan Ado Doguwa ko kuma tsoma baki a abin da ya shafe shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp