Alamun dumamar yanayi ne ya sa aka samu ruwan saman ba-zata a wasu jihohin arewacin Nijeriya - NiMet

Hukumar ta bayyana hakan ne a wajen wani taron kara wa juna sani da ta shirya wa ‘yan jarida tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniy na, wajen tunatar da ‘yan jarida kan dumamar yanayi ta yadda za su fadakar da al’ummar kasar nan.

Taron ya gudana ne a Otel din Rock Biew da ke Abuja, inda ta ce wannan wani sharar fage ne kan babban taron da aka fara a kasar Dubai daga ranar 30 ga Nuwamba zuwa 12 ga Disamba.

Hukumar NiMet ta yi nemi ‘yan jarida su kara kaimin fadakar da al’ummar Nijeriya kan illar dumamar yanayi a bangaren lafiya da tattalin arziki da kuma yadda za a magance matsalolin ta hanyar da ta dace.

A cewarta, ta dauki nauyin bayar da horo ga ‘yan jarida ne kan dumamar yanayi, saboda ayyukan ‘yan jarida ba zai iya misultuwa ba wajen fadakar da al’umma illarsa da kuma hanyoyin magance lamari.

Da yake jawabi a wurin taron, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya Mattias Schmale, ya ce dukkan kasashen duniya na fama da matsalar dumamar yanayi, amma kasashen da suka ci gaba sun dauki matakin rage matsalolin wanda hakan ya sa suke kokarin bayar da tallafi ga kasashe masu tasowa irinsu Nijeriya, domin a gudu tare a tsira tare.

Ya ce kididdiga ta nuna cewa kasashen Nahiyar Afirka su suka fi fuskantar barazanar kamuwa da illolin dumamar yanayi, wanda hakan  ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da hankali wajen taimaka musu.

Wakilin ya kara da cewa a 2023, an samu sauye-sauyen canjin yanayi ba ma a Nijeriya ba har da duniya baki daya, wanda akwai bukatar hada kannu da karfe wajen taimaka wa kasashe domin a tsira daga illar lamarin.

A tattaunawarsa da manema labarai, wakilin Kungiyar Masu Kula da Yanayi ta Duniya (WMO) a yankin yammaci da Afirika ta tsakiya, Mista Biyarnada Edward Gomez, ya bayyana cewa, an shirya taron ne don zaburar da ‘yan jarida da dukkan masu ruwa da tsaki wajen tattaunawa tare da bayar da rahotannin da suka shafi dumamar yanayi da yadda take addabar al’ummar sassan duniya da kuma irin gudunmwar da kowa zai bayar don rage irin matsalolin da ake fuskanta.

Ya ce, wannan yana da muhimmanci musamman da yake ana gudanar da babban taron ne da majalisar Dinkin Duniya ta shirya a kan dumamar yanayi a Hadaddiyar Daular Larabawa, taron shi ne na 28 tun da aka fara gabatarwa duk shekara.

“Muna zama ne a kan dumamar yanayi. Ana yin zaman saboda dumamar yanayi na addabar kowa a duniya. Kowa da kowa. Daga Nijeriya zuwa nahiyar Turai da Asiya da Amurka. Kuma babban abin da yake haddasa dumamar yanayi shi sinadarin CO2 din da suke fita wanda ni da kai duk muna taimakawa wajen gurbata muhalli. Idan kana tukin mota, motarka tana shan mai. 

Mai kuma yana fitar da sinadarin ‘Carbon Diodide’ cikin sararin samaniya idan kana amfani da ‘Air conditioner’ shi ma yana fitar da iskar. idan ka kunna wutar lantarki shi ma yana fitar da gurbatacciyar iska. Toh dukkanmu muna taimakawa wajen fitar da shi. Amma akwai kasashen da suka fi yi fiye da wasu, kasashen da suke da manyan kamfanoni, sun fi haifar da dumamar yanayi fiye da kananan kasashe”.

Mr Gomez ya kuma kara da cewa, “Dumamar yanayi na faruwa, me za mu yi a kai? Dole mu nemo hanyoyin da za mu saba. 
Misali, idan ana samun ruwa sosai da yake janyo ambaliya me za mu yi? Dole mu nemo hanyar da za mu saba. Ko kuma dalilin wannan zaman shi ne domin zaburar da ‘yan jarida domin su samu karfin gwiwa da ra’ayi a kan wadannan labarun, za su iya rubuta labarai a kan abubuwan da ke faruwa kuma su taimaka wajen sabawa da kuma shirya wa manyan dumamar yanayi, kuma muna kira gare ku ‘yan jarida ku sa ra’ayinku a kai, saboda wannan zai shafe ka kuma zai shafe shi kuma zai shafe ni, ya shafi dukkan al’umma.

Ya kara da cewa, “lallai mun yi sa’a, Nijeriya ba ma cikin manyan garuruwan da illolin dumamar yanayi yake shafa, idan ka samu kanka a garin da ake ambaliya sosai za ka iya rasa rayuwarka, zan iya rasa rayuwata. Saboda haka dukkanmu ya kamata mu maida hankali a kan abin da yake tafiya kuma mu fitar da labarun da za su tsawatar wa mutane don su dauki mataki a kan lokaci. Kuma a shirye muke mu ci gaba da ba ku wasu labarai da suka shafi dumamar yanayi don watsawa ga al’ummar yankunan karkara.”

Taron ya samu halartar masana daga cibiyoyin bincike, malaman jami’o’i da ‘yan jarida daga kafafen watsa labarai na jihohin Nijeriya da babban birnin tarayya Abuja.

Post a Comment

Previous Post Next Post