Buhari bai bar sisin-kwabo a lalitar gwamnatin Nijeriya ba - Nuhu Ribadu

Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya ce halin karancin kudin da gwamnatin Bola Tinubu ke fuskanta ya faru ne ta dalilin samun babu ko sisi a lalitar gwamnati a lokacin da ya hau kan karagar mulkin kasar watanni da suka gabata.

Sai dai Malam Nuhu Ribadu ya ce duk da halin da aka shiga na karancin kudin, gwamnatin tarayya na yin duk abin da ya kamata wajen ganin tsaron kasa ya inganta a sassan kasar nan.

Mai ba shugaban kasar shawara ta musamman ya yi wannan furucin ne a Abuja wajen taron hedikwatar tsaro na shekara-shekara.

Wannan taron dai ya samu halartar ministan tsaro Badaru Abubakar da karamin ministan tsaro Bello Matawalle da manyan hafsan sojin Nijeriya da sauransu.

Malam Nuhu Ribadu ya tabbatar wa da sojojin cewa gwamnatin tarayya ba za ta gajiya ba wajen ganin ta shiga ta fita don ta samar da kayan aiki don inganta tsaron kasa.

Ya ce "a zahirin gaskiya, muna fuskantar matsalar kudi. Ya kyautu in sanar da ku. Sannan yana da kyau ku sani cewa mun gaji wani matsanancin yanayi, abin da nake nufi, babu ko sisi a lalitar gwamnatin lokacin da muka karbi mulki".

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp