Babu wanda ya yi barazanar tsige Akpabio daga mukaminsa - Majalisa

Majalisar dokokin Nijeriya ta sa kafa ta shure wasu rahotannin da ake yadawa a kafafen watsa labarai cewa wasu fusatattun 'yan Sanatoci na shirin tsige shugabansu Sanata Godswill Akpabio.

Akwai wasu rahotannin da kafafen yada labarai suka watsa a ranar Asabar cewa ana shirin tsige shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio.

Rahotonannin sun ce akwai wasu Sanatoci da suka yi wata ganawa ta musamman a kasar Saudi Arabia don su kitsa yadda za a tsige Akpabio.

Sai dai, mai magana da yawun majalisar Yemi Adaramodu a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya bayyana wadannan rahotannin da cewa ba su da tushe bare makama.

Post a Comment

Previous Post Next Post