Za a samu matan da suka dauki juna biyu ba tare da sun shirya ba kimanin 700,000 cikin shekarar 2023 a Nijeriya

Asusun tallafa wa yawan al'umma na majalisar dinkin duniya UNPF ya ce kalubalen da ake fuskanta wajen shirin tsarin iyali na iya kaiwa ga yawan samun cikin-shege da yawan zubar da cikin.

UNPFA ta sanar da hakan ne a cikin sakonta na bikin zagayowar ranar yawan al'umma ta 2023 da hukumar kidaya ta kasa ta shirya a Abuja.

Kwararra a kan lafiyar mata masu juna biyu Dr Adeela Khan ta ce gibin da ale samu na ba da tallafin kudi wajen aiwatar da shirin tsarin iyali ya tashi daga Dala milyan 25 ya koma Dala milyan 32 a shekarar 2023.

A ta bakin Dr Adeela, wannan gibin kudin zai sa a samu juna biyu 700,000 da ba a yi niyyar samunsu ba da hakan zai sa a haifi cikunna 300,000 kuma a zubar da cikunna 300,000 a shekarar 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp