Tukur Mamu ya nemi a daukeshi daga hukumar DSS zuwa Kurkukun Kuje.

 Tukur Mamu ya nemi a daukeshi daga hukumar DSS zuwa Kurkukun Kuje.r

Wani wanda ake zargi da hannu cikin ayyukan bata gari a Nijeriya, Tukur Mamu,ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta dauke shi daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).


Ya roki mai shari’a Inyang Ekwo da ya sauya hukuncin daurin da aka yi masa na ci gaba da tsare shi a gidan yarin Kuje maimakon tsareshi a hukumar DSS.


A ci gaba da shari’ar, Mamu ta bakin lauyansa, Abdul Mohammed, ya yi zargin cewa umurnin da kotu ta bayar a ranar 19 ga watan Disamba, 2023 na a ba shi damar zuwa wurin likitansa domin jinya, ba a bi umarnin kotun ba.


A cikin takardar bukatar da Mohammed ya gabatar, Mamu ya yi ikirarin cewa an ba shi damar ganawa da likitan sau daya inda aka mika rahoton cikakken binciken lafiyarsa ga hukumar ta DSS.


Tun bayan gabatar da rahoton, Mamu ya yi zargin cewa ba a ba wa likitan damar zuwa wurinsa ba, don haka yana bukatar a yi masa tiyata cikin gaggawa a duk wani asibiti da ke gundumar.

Post a Comment

Previous Post Next Post