Ashirye nake na bayyana a gaban Kotu – Yahaya Bello
Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya roki wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta janye umarnin kama shi da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta (EFCC) ta yi masa a ranar 17 ga watan Afrilu.
Yahya Bello, ta bakin lauyansa Adeola Adedipe, SAN, ya gabatar da bukatar ne biyo bayan umarnin mai shari’a Emeka Nwite, inda ya umurci EFCC da ta aiwatar da tuhume-tuhumen da shaidu a kan babban lauyan tsohon gwamnan, Abdulwahab Mohammed, SAN.
Kamfanin dillancin labarai a Nijeriya NAN ya ruwaito cewa tun da farko mai shari’a Nwite, ya umarci lauyan EFCC, Kemi Pinheiro, SAN, da ta yiwa Mohammed babban lauyan Bello aike da tarin tuhume-tuhume da hujjojin shaida a hukuncin da aka yanke a yau.
Sai dai jim kadan bayan yanke hukuncin, Adedipe ya bayar da hujjar cewa umarnin kamawar, tun da aka bayar kafin tuhumar ya kamata a ajiye su a gefe yazo(da kansa, ba tare da wata bukata daga bangarorin da abin ya shafa ba).
Lauyan wanda ake tuhumar Adedipe,yace wanda ake tuhuma yana son zuwa kotu amma yana tsoron cewa akwai umarnin kama shi da ya rataya a kansa.