An cimma kaso 90% na jarjejeniyar gwamnati da 'yan kwadago- Minista
Ministar kwadago da samar da ayyukan yi a Nijeriya, Nkiruka Onyejeocha, ta ce gwamnatin kasar ta cimma kusan kaso 90% na yarjejeniyar da ta kulla tsakaninta da kungiyoyin kwadago tun a cikin watan Oktoban 2023.
Nkiruka is bayyana hakan ne a lokacin da take magana yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channels.
Onyejeocha ta ce shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (TUC), Joe Ajaero, ya shaidawa wakilan gwamnati a wani taro a ranar Lahadi cewa zanga-zangar da suka gabatar ba saboda jarjejeniyarsu da gwamnati ba ce, sun yi ta ne saboda tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyakn masarufi a fadin kasar baki daya.